SHUGABAN NAJERIYA YA LISSAFO ABUBU WANDA HARAJIN (VAT) BAZAI SHAFA BA. - HAUSA MEDIA24

People Online

Breaking

ads

Tuesday, 8 October 2019

SHUGABAN NAJERIYA YA LISSAFO ABUBU WANDA HARAJIN (VAT) BAZAI SHAFA BA.

 
   Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace Gwamnatinsa tagina kasafin kudinta bisa kan Harajin kaya da ake kira (VAT) Saboda haka zata kara Haraji akan ka yayyakin kasar daga kaso 5 zuwa 7.5. 
    Shugaba Buhari yace Dokar haraji VAT bazasu shafi magungunan kiwon lafiya da kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa…
    “A sashen na 46 da doka ta 2019, ta fadada ka yayyakin da Tsarin harajin VAT bazai shafa ba.
   Ka Yayyakin da Bazai shafa ba kuwa sune kamar Haka:-  
  1-Biredi fari ko ruwan kasa 
  2-Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa 
  3-Kifi da danginsa;
  4-Fulawa da abinci mai sitati; 
  5-Kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye 
  6-Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa
   7-Nama da kwai 
   8-Madara; 
   9-Gishiri da kayan kamshi
  10-Ruwa." 
    Hakanne zai baiwa gwamnatin damar cike gibi na sama da naira Trillion biyu wanda akasamu akan kasafin kudin Bara na 2019.
   Buhari wanda ya gabatar da Gaftaren kasafin kudin a gaban zauren majalisar dokokin kasar, ya ce kasafin na 2020 yafi na 2019 da kaso 9.7 cikin dari.
   Kasafin dai na 2019 ya kai naira tiriliyan 8.83, inda na 2020 zai wuce fiye da naira tiriliyan 10.
   Gwamnatin ta dogara da kasafin kudin 2020 ne a kan farashin gangar danyen mai dala 57, inda kuma ake hasashen Najeriyar za ta rinka fitar da gangar mai 1.86 a kullum ko wace rana.
   Yanda Kasafin kudin yagudana ga ma'aikatu da sassan gwamnati: 
   * Majalisar dokoki - naira biliyan 125 
   *Ma'aikatar Shari'a - naira biliyan 110
   *Aiki da gidaje - naira biliyan 262
   *Sufuri - naira biliyan 123 
   *Hukumar ilmin matakin farko ta UBEC - naira biliyan 112
   *Tsaro - naira biliyan 100
   *Aikin gona - naira biliyan 83 
   *Albarkatun ruwa - naira niliyan 82
   *Ilimi - naira biliyan 48 
   *Lafiya - naira biliyan 46
   *Hukumar Raya Arewa maso gabas - naira biliyan 38 
   *Birnin tarayya - naira biliyan 28 
   *Neja Delta - naira biliyan 24 
   *Ma'aikatar wutar lantarki - naira biliya 127 
   *Shirin gina yankunan kasa - naira biliyan 100
   *Masana'antu da zuba jari - naira biliyan 40 
   *Ma'aikatar cikin gida - naira biliyan 35 
   *Shirin tallafin ga 'yan kasa na Social Investment Programmes - naira biliyan 30 

No comments:

Post a Comment

ads1