Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yabayyana cewa akwai jahohin kasar dake fama da matsanancin Talauci, inda Shugaba Buhari yayi kira ga Antajirai da masu kudin kasar cewa sumaida hankali wajen kirkiro sana’o’i, bunkasa harkokin kasuwanci, cinikayya da gina kasa Najeriya ta hanyar yin amfani da arzikin da Allah yayi wa kasar.
Shugaban yayi wannan jawabine agurin taron Tattalin Arzikin kasar na karo 25 (NES25) da akeyi anan a babban Birnin Abuja, a Ranar litinin.
Shugaba Buhari yace Gwanatinsa zata ci gaba dayin Aiki Tukuru wajan Aiki da kamfanoni masu zaman kansu don bunkasa cigaban Tattalin Arzikin kasar baki daya.
SOURCES:PREMIUMTIMEHAUSA
No comments:
Post a Comment