SHAWARA: SAKO ZUWA GA MATAN SHUWA GABANIN MU - HAUSA MEDIA

People Online

Breaking

ads

Friday, 26 July 2019

SHAWARA: SAKO ZUWA GA MATAN SHUWA GABANIN MU


 
   Inaso zanyi amfani da wannan damar na isar da wani sako na musamman akan zaman takewarku da halattarku zuwa wajan Taro. Inaso zanyi tsokacine dangane da shigarku da Ado (dressing) wacce kukeyi ayayin wani gaggarimin biki ko taro asiyasance da ake gudanarwa dik shekara ko kuma karshen wata ko karshen Sati.
     Gaskiya shigarda kukeyi bata daya daga cikin kamala ko cancanta balan tana adangan tata da Addinin Musulinci saboda mafiyawanci bakwa kwai-kwayo da addinin (Musulinci) inde ta wannan fagenne kunsamu nakaso dakuma Gibi.
    Wannan ‘Dabi’ar taku tana cuwa al-umma tuwo a Kwarya, musamman idan mutum yatina cewa matar shugabansa tayi shigarda bata can-canci musulinciba sai yaji ransa yabaci kuma badadi.
    Tambaya wai shin Shuwa gabannin ne basa kishin matayesu ko kuma su matanne basa kishin mazajensu? Bayan haka laifin nasuwaye kuma hakkin akansuwa yake, Matan ko mazan? Shawara Hakika yakamata ace ku kyara Saboda zamowa abin kwai-kwayo acikin al-umma dama musulinci baki daya, rashin kyarawa, kalu balene Sosai arayuwar al-ummarmu, da ‘ya ‘ya yammu, dakuma jikoki.
   Saboda ita rayuwa darasine abin kwai-kwayo ce ga mutanan baya. Kusanifa cewa shigarku na kamala da daraja ita take nuni da zaman takewarku mai kyauce kuma abin sone da kwai-kwayo, bayan haka kutina da tambayar da Allah madaukakin Sarki zaiyi muku a ranar Gobe Giyama, Shin kunyita Mai kyau kamar yanda yace ayi ko kuma kunsabamar kunyi Son ra’ayinku.
   Daga karshe ina baku shawara akan kyara wannan Dabi’artaku, tazama irin na kamala da daraja kuma gwanin sha’awa da birgewa, irin na Musulinci da Musulmai.
 
   Bissallam Allah yabaku ikon kyarawa Ameeeeen.

No comments:

Post a Comment

ads1