AIYUKA GUDA BIYAR NA DAREN LAILATUL QADRI - HAUSA MEDIA

People Online

Breaking

ads

Wednesday, 29 May 2019

AIYUKA GUDA BIYAR NA DAREN LAILATUL QADRI

*_AIYUKA GUDA BIYAR NA DAREN LAILATUL QADRI_*.

Ayyukan Da Ake Son Yi A Daren Lailtul Qadri

*1-I'itikafi*
Ana yinsa ne a goman qarshe a Ramadan,ba sai a daren Lailatul Qadri kadai ba,kuma babban dalilinsa shine dan Dacewa da Lailatul-Qadri.

An karbo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce,
*(Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya kasance yana yin I’itikafin kwanaki goma na qarshe a Ramadan)*
@Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

*2-Tsayuwa a wannan dare don imani da neman lada*

Tsayuwar dare ya kushi
*Sallah*
*Tuba da Istighfari*
*Addu'a da Azkar*
*Karatun Alqurani*.

Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce;
*(Wanda ya yi tsayuwa daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)*
@Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

*3-Addu'a*
An karbo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, na ce, ya Rasulallahi, idan na dace da daren Lailatul Qadri, me zan yi addu’a da shi? Sai ya ce, ki ce, _“Allahumma Innaka Afuwwun Karimun Tuhibbul Afwa Fa’afu Anni”_
 Ma’ana
*“Ya Allah kai mai afuwa ne mai karamci,kana son afuwa, ka yi min afuwa”*
@Tirmizi ne ya rawaito shi.

*4-Tayar da iyali suyi Ibada*
Manzon Allah SAW idan kwanakin goman karshe ya shigo yana kara degewa da ibada kuma yaka tayar da iyalinsa suma suyi ibada.
@Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi


*5-Tuba daga zunubi yawaita Istighfari*

Manzon Allah SAW yana cewa:-
*(A kowane dare idan kashe ukkun karshe ya shigo Allah yana saukowa zuwa samar duniya yana cewa,wa zai rokeni na bashi,wa zai tambayeni na amsa masa,wa zai nemi gafarata na gafarta masa)*
@Saheehul Jami'i


Allah ne mafi sani*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ*
_“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa’afu anni”_

No comments:

Post a Comment

ads1